Ana zargin ’yan bindiga a kan hanyar Okene da yin garkuwa da wani mutum mai suna Mista Mike Oguguo Ndu daga Anambra tare da wasu matafiya.
Mista Ndu, wanda tsohon dan jarida ne ya hau motar haya ne domin ziyartar matarsa da ba ta da lafiga a Abuja.
- An yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kogi
- ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 17 a Kogi
Motar ta baro Onitsha zuwa Abuja ne a ranar Litinin da misalin karfe 7:20 na safe.
Tun bayar tasowarsa yake waya da iyalansa, amma misalin karfe 3 na yamma aka daina samunsa a waya.
Sai a ranar Talata ne aka kira dan uwansa Joseph Ndu, aka bukaci Naira miliyan 50 kudin fansa.
Bayan faruwar lamarin iyalansa sun je kamfanin motocin WAZOBIA da ke Gwagwalada a Abuja, inda Manajan kamfanin ya ce za a taimaka musu da bayanan da suke da shi game da batan mahaifin nasu.
Mike Ndu mai shekara 70 yana fama da matsanancin ciwon suga da hawan jini, yanayin da ke iya ta’azzara a hannun masu garkuwar.
Kafin Mista Ndu ya yi ritaya, ya yi aiki da kamfanin jarida Monitor da mujallar Enterprise da ke Oyo; gidan rediyon Madonna FM da ke Okija sai kuma jaridar The Nation a Onitsha.