✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mai shekara 55 a Jigawa

’Yan bindigar sun yi batar dabo da mutumin da suka dauke a Ringim.

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani mutum mai suna Hamidan Habu a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa,  ASP Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan a Dutse a safiyar Laraba.

  1. Yunwa ta sa daliban sakandare zanga-zanga a Gombe
  2. ’Yan bindiga sun sace mata 60 a Zamfara

“Ranar 6 ga Yuni da misalin karfe 1:30 na dare, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Hamidan Habu mai shekara 55, a kauyen Shengel da ke Ringim zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Sai da suka yi harbe-harbe a iska kafin su tafi da shi daga kauyen da ke da nisan kilomita 25 da garin Ringim,” a cewar Shisu.

Daga baya jami’an ’yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka gano fankon harsashi.

A cewar kakakin, ’yan sandan na ci gaba da bincike tare da bin sahun wadanda suka yi awon ga a da mutumin don cafke su.