✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mai jego an bar jaririnta

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yar jarida mai jego suka yi watsi da jariririnta.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wata ’yar jarida mai jego suka yi watsi da jariririnta.

’Yan bindigar sun kutsa gidan Amra Ahmad Diska, Edita a Hukumar Yada Lababarai ta Jihar Adamawa (ABC) ne da dare, suka tafi da ita, amma suka bar jaririn mai wata shida da haihuwa a gida.

“Da alamar ’yan bindigar sun je ne da nufin yin garkuwa da mijin ’yar jaridar amma da ba ba su same shi ba, sai suka tafi da mai jegon‚” inji wani shaida, wanda ya ce lamarin ya faru ne kafin wayewar garin Talata.

Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya ce an yi garkuwa da ’yar jaridar ce da misalin karfe 1 na dare a gidanta da ke  unguwar Mamba a wajen garin Yola.

DSP Nguroje ya ce tuni aka tura jami’ai su bi sawun masu garkuwar, kuma yana da kwarin gwiwar cewa za a kama su, su fuskanci hukunci.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, majiyoyi masu kusanci da iyalan Amra sun ce masu garkuwar ba su tuntube su ba tukuna.

%d bloggers like this: