’Yan bindiga sun yi garkuwa da wata ’yar jarida mai jego suka yi watsi da jariririnta.
’Yan bindigar sun kutsa gidan Amra Ahmad Diska, Edita a Hukumar Yada Lababarai ta Jihar Adamawa (ABC) ne da dare, suka tafi da ita, amma suka bar jaririn mai wata shida da haihuwa a gida.
- An kara sako dalibin Jami’ar Greenfield
- An yi garkuwa da Shugaban Miyetti Allah na kasa
- An kori kwamandan Hisbah da aka kama da matar aure a otal
- Sakin aure da suka fi cin kudi a duniya
“Da alamar ’yan bindigar sun je ne da nufin yin garkuwa da mijin ’yar jaridar amma da ba ba su same shi ba, sai suka tafi da mai jegon‚” inji wani shaida, wanda ya ce lamarin ya faru ne kafin wayewar garin Talata.
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya ce an yi garkuwa da ’yar jaridar ce da misalin karfe 1 na dare a gidanta da ke unguwar Mamba a wajen garin Yola.
DSP Nguroje ya ce tuni aka tura jami’ai su bi sawun masu garkuwar, kuma yana da kwarin gwiwar cewa za a kama su, su fuskanci hukunci.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, majiyoyi masu kusanci da iyalan Amra sun ce masu garkuwar ba su tuntube su ba tukuna.