✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mahaifiyar dan majalisa a Kano

Mahara sun yi amfani da karfin tuwo suka karya kofar gidan mahaifiyar dan majalisar.

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Mazabar Gezawa, Isyaku Ali-Danja.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai hari gidan mahaifiyar dan majalisar da ke garin Gezawa ne da misalin karfe 1 na daren ranar Talata, suka balla kofar gidan sannan suka yi awon gaba da ita.

Ali Danja, wanda tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ne, ya ce maharan sun yi amfani da karfin tuwo wajen karya kofar gidan sannan suka sace mahafiyarsa.

Ya ce bayan maharan sun bar garin ne wata tsohuwa ta yi shela tare da shaida wa jama’a abin da ya faru.

“Kafin in karasa Gezawa ’yan sandan da ke Gezawa sun kira suka tabbatar min cewa an aike da karin jami’an tsaro zuwa gidan domin gudanar da bincike.

“Har yanzu ba mu ji daga gare su ba. Muna rokon Allah Madaukakin Aarki Ya kubutar da ita,” a cewarsa.

Sai dai har muka kammala hada wannan rahoton Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ce komai dangane da faruwar lamarin ba, sannan bai daga wayar wakilinmu ba ballantana a ji ta bakinsa.