Wasu mahara da ba a san adadinsu ba sun sace akalla mutum takwas ma’aikatan kamfanin aikin yumbu da ke Karamar Hukumar Ajaokuta a Jihar Kogi.
Maharan sun yi awon gaba da ma’aikatan a kauyen Emirowo da ke kan hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta.
- Lasisin tuka Adaidata Sahu ya koma N100,000 —KAROTA
- Ya shiga hannu bayan tserewa da motar makarantar da yake aiki
Aminiya ta ruwaito cewar ma’aikatan sun shiga hannun ’yan bindigar yayin da suke tsaka da aiki a garin na Ajaokuta.
Har yanzu ba wata masaniya game da inda maharan suka kai ma’aikatan bayan sace su, amma daya daga cikin matan ma’aikatan, mai suna Hassan Shu’aibu ta tabbatar da sace mijinta.
Ta ce “Tabbas, mijina na cikin wanda aka yi garkuwa da su a Emirowo. Har yanzu ba mu san halin da suke ciki ba. Ni yanzu haka a rude nake ban san abin da zan yi ba.”
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Williams Ovye ya tabbatar da faruwar lamarin yammacin ranar Laraba.
Sai dai ya ce mutum shida ne ma’aikatan kamfanin aikin yumbu aka sace.
A cewarsa, hadin gwiwar jami’an tsaro a jihar na fadada bincike don ganin sun ceto mutane da aka sace.