’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani alkalin Kotun Shari’ar Musulunci a kauyen Bauren Zakat da ke yankin Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
Ganau sun shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kutsa cikin zauren kotun da misalin karfe 3 na ranar Talata, suka sace alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama’ila.
- ’Yar shekara 6 ta mutu sakamakon fyade a Kaduna
- Matakan nada Khalifan Tijjaniyya — Sheikh Dahiru
- Ya yi aure sau 4 ya saki matar sau 3 cikin kwanaki 37
An sauya wa kotun matsuguni zuwa garin Safana saboda dalilai na tsaro.
Babu tabbas kan dalilin da alkalin ya halarci kotun a daidai lokacin da ma’aikatan shari’ah ke yajin aikin Kungiyar Maáikatan Shari’ah na Qasa, JUSUN, ke yajin aiki.
Kungiyar JUSUN din ta tsunduma yajin aiki tun ranar 6 ga watan jiya, domin neman aiwatar da tanadin sashi na 81(3), da sashi na 121(3) da ma sashi na 162(9) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara) kan ’yancin alkinta kudade ga bangaren sharia’ar a matakan jihohi.
Jihar Katsina dai ta kasance guda cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma inda ’yan bindiga ke cin duniyarsu da tsinke.
Sai dai har zuwa lokacin rubuta labarin, jami’an tsaro ba su ce uffan game da lamarin sace alkalin ba.