Wasu alkalai biyu na kotun shari’a ‘yan jihar Zamfara, sun fada tarkon masu ta’adar garkuwa da mutane yayin da suke kan hanyar dawo wa daga wata tafiya da suka yi zuwa kasar Nijar a ranar Juma’a, 11 ga watan Satumba.
Alkalan biyu, Sabi’u Abdullahi da Shafi’i Jangebe, sun yi gamo da wannan tsautsayi yayin da suke hanyarsu ta dawo wa daga wani taro da suka halarta a garin Maradi da ke makociyar kasar.
Har ya zuwa lokacin da tsautsayin ya auku, Sabi’u shi ne na’ibi ga babban limamin Masallacin Usaimin da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
- Gwamnan Yobe ya yi alhinin mutuwar diyar Wamakko
- Dan sanda ya lakada wa budurwa dukan da ya yi ajalinta
Babban limamin masallacin Umar bin Khaddab na babban birnin jihar, Umar Kanoma, shi ne ya tabbatar da lamarin yayin gabatar da hudubarsa ta Juma’a.
Shaikh Kanoma ya nemi daukacin al’ummar musulmi da su sanya alkalan biyu cikin addu’o’insu na neman Mai Duka ya jibinci lamarinsu.
‘‘Muna neman barar addu’o’i daga musulmai da sauran jama’a don a saki alkalan da aka dauke a hanyarsu ta dawo wa daga Maradi na jamhuriyyar Nijar,’’ inji shi.
Haka kuma limamin ya kirayi gwamnati da ta tashi ta farga wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.
A yayin neman jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba ballanta kuma sakon tes da aka tura masa.