✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkurwa da babban dan sanda a Kwara

Hukumar ’Yan Sandna ta ce, “Tabbas gaskiya ne, amma muna kan aiki a kan lamarin.”

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani hafsan dan sanda mai mukamin Mataimakin Sufirtanda, (ASP) Abdulmumini Yusuf, a yankin Ilori, babban birnin Jihar Kwara.

Aminiya gano cewa a ranar Talata da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da ASP Abdulmumini a lokacin da yake kokarin shiga gidansa a unguwar Ogidi da ke garin Ilori.

A ranar Alhamis Kwamishinan ’Yan Sandna Jihar Kwara, Paul Odama, ya ce, “Tabbas gaskiya ne, amma muna kan aiki a kan lamarin.”

Kakakin rundunar, SP Okasanmi Ajayi, ya ce babu cikakken bayani game da yadda abin ya farku, amma duk da haka, suna aika kai da fata domin ceto hafsan dan sandan da ’yan bindiga suka sace.

Wani mazaunin unguwar Ogidi mai suna Jamiu Abdulganiy ya ce sace dan sandan ya jefa yankin cikin zullumi da mamaki.

Amma kakakin ’yan sandan jihar, SP Ajayi, ya ce, “Duk da girman abin da ya faru, hakan bai sanyaya wa rundunarmu gwiwa ba a aikinmu na kare rayuda da dukiyoyin jama’a.