✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi canjaras tsakanin Algeria da Burkina Faso a Gasar AFCON

Yanzu dai Burkina Faso da Angola ne a saman teburin rukunin D kowanne da maki hudu-hudu.

Algeria da Burkina Faso sun tashi da canjaras 2-2 a wasan da suka barje gumi a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON da gudana a Ivory Coast.

Dan wasan Burkina Faso, Mohamed Konate ne ya fara zura kwallo a ragar Algeria gab da za a tafi hutun rabin lokaci a fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade de Bouake.

Sai dai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne dan wasan Algeria Baghdad Bounedjah ya farke kwallon a minti na 51.

A cikin minti na 70 ne kuma Burkina Faso ta sake samun wata damar, inda dan wasanta Bertrand Traore ya zura kwallo ta biyu a ragar Algeria ta hanyar bugun fenariti.

Sai dai murnar ‘yan wasan Burkina Faso ta koma ciki bayan da Bounedjah ya zura kwallo ta biyu a ragarsu.

Yanzu dai Burkina Faso da Angola ne a saman teburin rukunin D kowanne da maki hudu-hudu, inda ita kuma Algeria ke biye da su da maki biyu, sai Mauritaniya wadda Angola ta lallasa da 2-3 a kasan tebur babu maki ko daya.