Algeria da Burkina Faso sun tashi da canjaras 2-2 a wasan da suka barje gumi a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON da gudana a Ivory Coast.
Dan wasan Burkina Faso, Mohamed Konate ne ya fara zura kwallo a ragar Algeria gab da za a tafi hutun rabin lokaci a fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade de Bouake.
- Iyaye 106 sun tsere sun bar ’ya’yansu a Gombe — Human Rights
- Arsenal ta yi wa Crystal Palace raga-raga a Emirates
Sai dai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne dan wasan Algeria Baghdad Bounedjah ya farke kwallon a minti na 51.
A cikin minti na 70 ne kuma Burkina Faso ta sake samun wata damar, inda dan wasanta Bertrand Traore ya zura kwallo ta biyu a ragar Algeria ta hanyar bugun fenariti.
Sai dai murnar ‘yan wasan Burkina Faso ta koma ciki bayan da Bounedjah ya zura kwallo ta biyu a ragarsu.
Yanzu dai Burkina Faso da Angola ne a saman teburin rukunin D kowanne da maki hudu-hudu, inda ita kuma Algeria ke biye da su da maki biyu, sai Mauritaniya wadda Angola ta lallasa da 2-3 a kasan tebur babu maki ko daya.