Ma’abota dandalin sada zumunta na Facebook sun yi ta ce-ce-ku-ce bayan wata mata ta bayyana yadda ta yi cinikin kuli-kuli na Naira biliyan daya a shekarar 2022 da ta gabata.
Matar mai suna Angela Job Emodiae ta yi ikirarin sayar da kuli-kuli na Naira biliyan daya a bara inda kuma ta ke fatan rubanya cinikinta a bana.
- 2023: Dalilina na janyewa daga takarar dan majalisa — Alan Waka
- ‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara
Ta yi ikirarin ne a shafinta na Facebook inda ta ce:“Na sayar da kuli-kuli na Naira biliyan daya a shekarar 2022 ina fatan yin cinikin biliyan biyu a wannan shekara ta 2023.”
Sai dai kuma bayan shan suka daga mutane a kafar ta Facebook ta fito ta bayyana cewa rubutun da ta wallafa a baya ba gaskiya ba ne wasa ne take yi.
Har wa yau ta kara da cewar, ta yi ikirarin ne don ta ja hankalin mutane a dandalin na Facebook amma tana fatan samun cinikin da ya wuce na bara a bana.
Wannan ya sa wadanda suka bayyana kokwanto kan yiwuwar samun cinikin Naira biliyan daya a sana’ar kuli-kuli suka koma zolayar wadanda suka fara kare maganar a karon farko da cewa sam dama ba abin da zai yiwu ba ne.