Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Wayar Hannu da aka fi sani da Kasuwar Jagwal a birnin Damaturu na Jihar Yobe, ta lashe dukiya ta akalla Naira miliyan 150 a wannan Talatar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Damaturu, jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe, Malam Baba Bello, ya ce akalla shaguna 30 ne gobarar ta lalata.
- Ba ni da shirin sauka daga gadon sarauta — Sarkin Norway
- Marigayiya Nabeeha ta kammala Jami’ar ABU da ‘1st Class’
“Da misalin karfe 5:50 na safiyar Talatar, mun samu kiran gaggawa ana sanar da mu faruwar lamarin.
“Bayan ’yan mintuna kaɗan tawagar jami’anmu ta isa wurin, amma kafin isarta wutar ta riga ta yi karfi,” in ji Baba Bello.
Bello ya kara da cewa bincike ya nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon karuwar karfin wutar lantarki da aka samu a yankin a ’yan kwanakin nan.
Ya shawarci al’umma da ’yan kasuwa da su riƙa kashe duk kayayyakin gidansu ko shaguna da zarar za su fita ko kuma sun tashi daga kasuwa.
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Damaturu, Alhaji Ali Sheriff, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar kayayyakin da suka kai akalla Naira miliyan 150.
Shi ma Alhaji Sheriff ya bayyana cewa akwai yiwuwar wutar lantarki ce ta haddasa wannan gobarar.
“Da sanyin safiyar wannan Talatar aka kira ni a kan abin da ke faruwa, kuma muka garzaya wurin da lamarin ya faru don ganewa idan mu wannan iftila’i.”
Alhaji Ali ya ce jami’an ‘yan sanda sun ba da gudunmawar hana satar kayayyakin ‘yan kasuwar da idan irin haka ta faru wasu batagari ke yi amfani da wannan damar.
Haka kuma, wani mai sayar da hatsi da suka haɗa da gero da dawa a kasuwar, Malam Yahya, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar jimillar buhu 130 a sakamakon afkuwar lamarin.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su kawo agaji ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa don rage musu raɗaɗin wannan iftila’i da ya afka musu.
Shi ma Malam Musa Usman, wani dan kasuwar ya roƙi Gwamnatin Yobe da kuma Hukumar Agaji Gaggawa ta Jihar SEMA da su gaggauta kawo musu ɗauki domin samun sauƙin lamarin.