✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi Abuja da gawar Marigayi Ibrahim Attahiru

Ana dakon isowar gawar Babban Masallaci na Abuja domin jana’izar.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauki gawar Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru daga Kaduna zuwa Abuja, inda za a yi mata jana’iza.

Wata majiyar soji wacce ta inganta rahoton, ta ce yanzu haka jami’an tsaro na dakon isowar gawar Babban Masallaci na Abuja domin jana’izar.

Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ne ya yi dakon gawawwakin Janar Attahiru da sauran jami’an da ajali ya katse musu hanzari yayin hatsarin jirgin saman da ya ritsa da su ranar Juma’a a Kaduna.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, ayarin dakarun soji cikin jerin gwanon motoci ne suka yi rakiyar gawar Babban Hafsan Sojin Kasan daga Asibitin Sojin Kasa da ke Kaduna zuwa Filin Jiragen Sama na rundunar Sojin Sama da ke Mando.

Aminiya ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce da misalin karfe 12.30 za  ayi jana’izarsa madadin karfe 10 na safiya da aka sanar a baya.