Wata kotu a kasar Libya ta yanke wa wasu ’yan kungiyar IS su 17 hukuncin kisa.
Dukkansu an same su da aikata laifuffuka a lokacin da masu ikirarin jihadi suke da iko da Yammacin Sabratha.
Ofishin Babban Mai shari’a na kasar ya ce mutanen na da hannu a kisan mutane fiye 50 da kuma sace wasu dama.
Kungiyar IS ta kwace ikon wasu yankunan Sabratha a 2014, kafin daga bisani ta kwace ikon birnin Sirte, wanda ya zamo matattarar masu ikirarin jihadin a Libya.
Bayan shekara biyu da kwace ikon, sojojin Libya da ke biyayya ga gwamnatin kasar sun fatattake su daga birnin.(RFI)