Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jihar Kano kan laifin aikata kisa a wurin bikin ɗaurin aure.
Babbar Kotun Jihar Kano ta kuma yanke wa matashin mai suna Abba Suleiman hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari kan laifin hada baki da aikata laifi.
Mai Shari’a Amina Adamu ta yanke wa Abba hukuncin ne tare da wasu abokansa da suka tsere, bayan samun su da laifin caka wa wan mai suna Iliyasu Tasi’u wuka har lahira a yayin bikin auren.
An fara gurfanar da Abba a kotun ne 2019 bayan an kama shi yana ƙoƙarin hana kai wata amarya dakin mijinta a unguwar Sauna Kawai da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar.
A lokacin taƙaddamar ce wanda a ake zargin ya aikata kisan da aka yanke masa hukumci a kai.
Bayan sauraron lauyoyi da shaidun masu kara da wanda ake ƙara, Alƙali Amina Adamu ta ce masu kara sun gabatar da gamsassun dalilai da ke tabbatar da laifin wanda aka gurfanar don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma ɗaurin shekara biyar.