Wani matashi dan shekara 23 mai suna Iniobong Moses, ya yanki tikitin zama a gidan dan kande har na tsawon rayuwarsa bayan wata Kotu ta kama shi da laifin yi wa agolarsa ’yar shekara 3 fyade.
Kotun ta zartar wa da matashin hukuncin daurin rai da rai bayan ya yi ikirarin sanya yatsunsa da kuma azzakarinsa cikin farjin ’yar kankanuwar yarinyar yayin da mai dakinsa ta fita cefane kasuwa a ranar 8 ga watan Nuwamban 2019.
- Majalisar Zartarwa ta amince da kudirin tsawaita shekarun ritayar malamai
- Shugaban Amurka Joe Biden da Kamala Harris sun karbi rantsuwa
- Auren Mata dubu: An daure malami shekara dubu a Turkiyya
Sai dai matashin wanda mazauni ne a Unguwar Afaha Udo Eyop da ke Karamar Hukumar Asutan ta Jihar Akwa Ibom, ya ce ya aikata laifin ne yana cikin maye.
Binciken da kwararrun kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewa matashin ya yi wa agolarsa lahani a gabanta tare da shafa mata wasu cututtuka a farjin nata.
Da yake zartar da hukunci ranar Laraba a babbar kotun ta Uyo, Jastis Okon Okon ya samu matashi da aikata laifin fyade da ake tuhumarsa wanda a cewarsa ya saba wa sashe na 367 cikin kundin dokokin manyan laifuka na Jihar Akwa Ibom.
Jastis Okon ya misalta matashin a matsayin abun kunya ga al’umma wanda a cewarsa laifin da ya aikata ya cancanci marbata kasa da ta dabbobi.
Ya ce matashin da ake tuhuma bai cancanci ya ci gaba da yawo a doron kasa ba ballanta shakar iskar ’yanci da rayuwa tare da al’umma nagari ba.
Kotun ta kuma yi watsi da ikirarin matashin na cewa ya aikata laifin yana cikin maye, inda ta ce, “shari’a ba ta la’akari da kasancewar mutum cikin maye yayin aikata kowane nau’in miyagun laifi saboda haka ba hujjarsa ba za ta karbu.”
Kotun ta kafe a kan cewa, Moses ya cancanci a kawar da shi na tsawon lokaci daga cikin al’umma domin tseratar da yarinyar daga wani karin tozarci da ya sanya ta a ciki.”