✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yanke wa matashi daurin wata 9 saboda satar waya

Dubun matashin ta cika lokacin da ya kokarin sake aikata sata a kasuwa.

Wata kotu da ke zamanta a yankin Gwagwalada a Abuja, ta yanke wa wani matashin manomi, Sadiq Ismaila daurin wata tara a gidan yari sakamakon hali bera.

Matashin wanda dan asalin kauyen Shaku ne da ke Lambata a Jihar Neja an same shi da laifin satar wayar salula.

Alkalin kotun, Sani Umar ya yanke wannan hukunci ne bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da neman afuwar kotun.

Sai dai alkalin, ya ba shi damar biyan tarar kudi har N40,000 ko kuma a tisa keyarsa zuwa gidan Dan Kande.

Kazalika, ya umarci matashin da ya biya wanda ya shigar da karar, Ahmed Mohammed N53,000.

Mai gabatar da kara, Mr Abdullahi Tanko, ya shaida wa kotun cewa tun da farko dai ma wayar salular, Ahmed Mohammed wanda ke zaune a Unguwan Dodo a yankin Gwagwalada na Abuja, ya shigar da kara a ofishin ‘yan sandan na Gwagwalada a ranar 28 ga watan maris.

Ya bayyana yadda wanda ake tuhumar ya je yankin na Gwagwalada a watan Fabrairu ya kuma sace masa waya kirar Infinix wanda kudinta ya kai kudi N53,000.

Ya kara da cewa ya sayar da wayar kan kudi N23,000 sannan ya yi bushashar gabansa da kudin.

Tanko, ya kara da cewa wanda ake tuhumar dubunsa ta cika, yayin da yake yunkurin sake yin wata satar a kasuwa.

Ya ce laifin ya saba da sashe na 287 na kudin laifuka na ‘Penal Code’.