✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yanke wa mai kamfanin Crypto daurin shekara 11,196 a Turkiyya

Kotu ta yanke wa shugaban kamfanin kudin Crypto na Thodex hukuncin daurin shekaru 11,196,

Kotu ta yanke wa shugaban kamfanin kudin Crypto na kasar Turkiyya hukuncin daurin shekaru 11,196, kan laifin damfara da safarar kudaden haram.

An yanke wa Faruk Fatih Ozer shugaban kamfanin Thodex, tare da ’yan uwansa biyu, kowannensu hukuncin daurin shekaru 11,196 ne a ranar Alhamis, bayan durkushewar kamfanin.

Kotu ta sami Faruk Fatih Ozer, mai shekaru 29 da laifin zamba, kafa kamfani aikata laifi da kuma safarar haramtattun kudade.

Masu shigar da kara sun je kotu ne suna neman a yanke masa hukuncin daurin shekaru 40,562, bisa samunsa da laifin almundahana da zamba da kuma kafa kungiyar masu aikata laifuka.

Amma kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito Ozer yana shaida wa kotun cewa, “Idan da kungiyar masu aikata laifuka zan kafa da, da ban zan yi da rashin kwarewa ba.”

Turkiyya dai ta yi kaurin suna wajen yanke wa mutane da yawa hukuncin dauri irin daya, wanda ya zama ruwan dare bayan da kasar ta soke hukuncin kisa a shekarar 2004 don samun shiga Tarayyar Turai.

Tun da farko an ya zargin Ozer ya tsere daga Turkiyya da Dala biliyan biyu na masu zuba jari, ko da yake akwai takaddama kan yawan kudin.

Amma masu gabatar da kara sun ce Ozer ya tura Lira miliyan 250 (kimanin Dala miliyan 30) na kadarorin masu zuba jari zuwa wasu asusun sirri guda uku a lokacin da ya tsere daga Turkiyya, kuma yawancin kudaden ya tura ne zuwa banki a kasar Malta.

’Yan uwan nasa kuma, Serap da Guven, an same su ne da laifin jawo wa masu zuba jari asara ta Lira miliyan 356.

Ozer ya kara samun shuhura ne bayan da aka ga hotonsa yana ganawa da wasu jiga-jigan masu goyon bayan gwamnati.

A shekarar da ta gabata aka kama a kasar Albaniya bisa sammacin kama shi na kasa da kasa daga Interpol.

Shari’arsa ta dauki hankali a Turkiyya, kasancewar ta zo ne daidai lokacin da harkar crypto ke habaka a kasar, bayan a baya harkar ta yi kasa saodai saboda tsauraran dokokin gwamnati.

Turkawa sun fara rungumar kudaden crypto ne matsayin kariya daga asara bayan karyewar darajar Lira da ta fara sama da shekaru 20 da suka gabata.