Kotu ta yanke wa wani mai shekara 59 hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin yi wa wani yaro mai shekaru hudu.
Mai shari’a Eno Isangedighi, na Babbar Kotun Jihar Anambra ya yanke wa Pius Udo Ben, mai ’ya’ya bakwai hukuncin kisa ne, kan laifin sace yaron a lokacin da yaron ke barci a shago mahaifiyarsa.
“Kotu ta yanke maka kai, Pius Udo Ben hukuncin kisa ta hanyar rataya, har sai ranka ya fita,” in ji alkalin a lokacin da yake yanke hukuncin.
Kotun ta ce a shekarar 2014 ne mutumin da wani dan acaba da ke nema ruwa a jallo suka yaudari yayar yaron mai shekaru 11 ta bar shagon domin sayo kifi.
Ko da ta dawo sai ta samu dan uwan nasa ya yi layar zana tare da wanda ake zargin.
A sakamakon haka ne mai garin kauyen Iko da ke Eket ya umarci daukacin mazauna kauyen su yi layi, inda yarinyar ta gano ta kuma nuna wanda ya sace kanen nata..
Mai shari’a Eno Isangedighi, ya kama Pius Udo Ben da laifi ya kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.