✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu gadi kan yi wa ’yar shekara 12 fyade

An kama masu gadin da suka yi wa ’yar shekara 12 ne bayan mahaifiyarta ta kai kara ofishin ’yan sandan yankin.

An cafke wasu masu gadi kan zargin hadin baki da yi wa wata karamar yarinya a gidan da suke aiki fyade a yankin Kirikiri da ke Jihar Lagas.

’Yan sanda sun kama masu gadin da suka yi wa ’yar shekara 12 ne bayan mahaifiyarta ta kai kara ofishin ’yan sandan yankin.

Kakakin ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce mahaifiyar yarinyar ta kawo kara cewa ’yarta ta kasa barci saboda abin da masu gadin gidansu suka yi mata a dakinsu.

Hundeyin ya ce mahaifiyar ta shaida musu cewa, “bayan da ta kai ’yar kemis ne ta shaida mata cewa daya daga cikin masu gadin nasu ne ya nemi ta taimaka masa da abinci, a lokacin da ta sauko daga bene.

“Da ’yar ta kawo masa abincin sai ya yaudare ta zuwa dakin masu gadi, inda abokin aikinsa kuma ya rika lura da motsin mutane, aka yi mata fyaden a dakin.

“Ta ce ’yar tata ta sume a cikin dakin, inda bayan ta farfado aka gano an yi mata fyade.