✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yanke wa dan damfara daurin shekara 235 a Oyo

Kotun ta same shi da laifuka 45, wanda hakan ya sa ta yanke masa hukunci.

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 35 a gidan gyaran hali, kan laifin zamba cikin aminci.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a ranar 2 ga watan Yuli, 2019, karkashin jagorancin Mai Shari’a Jude Okeke na Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Oyo.

EFCC ta zarge shi da laifuka 45 da suka hada da sata, halasta kudin haram, damfarar yanar gizo da kuma hadin baki, wadanda suka sa kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara 235.

Da farko wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifukan da ake zargin sa, lamarin da ya sanya shari’ar daukar tsawon shekaru ana yi.

Daga bisani, alkalin ya ce ya gamsu da hujojjin da aka gabatar wa kotun inda ya ce ta sami wanda ake zargin da laifi sannan ta yanke masa hukuncin daurin.

Kotun ta ce laifin ya saba da sashe na 321(1) na kundin laifuka na Jihar Oyo na shekarar 2003.

%d bloggers like this: