Wasu da ake zargin matsafa ne sun yanke mazakutar wani malamin makarantar allo ana daf da daura masa aure a gundumar Awai da ke Karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.
An yi wa Alaramma Salisu Mai Almajirai yankan rago aka yanke masa mazakuta a hanyar da da dawowa daga karbo kayan shiga angoncinsa.
Da yake zantawa da Aminiya, Sarkin Gundumar Awai, Rufa’i Waziri, ya ce sun shiga tashin hankali kan tsintar gawar Alaramma Salisu a yashe a ne gefen hanyar zuwa cikin garin na Awai.
Sarkin ya kara da cewa shi a lokacin da aka tsinci gawar Alaramma Salisu Mai Almajirai, wadda ko da aka duba sai aka ga cewar an cire masa mazakuta.
- An kama matar da ta sayar da kananan yara 42
- Hankalin jama’a na daɗa tashi saboda tsadar kayan abinci
Basaraken ya kara da cewa shi marigayin Alaramma Salisu ba shi da abokin fada a garin, kowa ya san cewa mutumin kirki ne, don haka kisan gialla da aka yi masa ya girgiza mutanen yankin baki dayansu.
Basaraken ya ce suna rokon Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan kisa.
Matar marigayin, Malama Zulaihat ta shaida wa wakilinmu cewa ranar Laraba da safe suka rabu, “bayan ya sayo wa yara kosai, sai ya ce zai je tsohon gidan da muka taso ya gaishe da mai gidan. To daga nan sai al’majirai suka shigo suka ce malam ya wuce zuwa Zariya.”
Ta kara da cewa “to da ma yana shirin kara aure ne, don haka ya je karbo dinkin shigar angonci ne a Zariya.
“To da yamma ta yi bai dawo ba, sai na aika aka kira mun budurwar da zai aura cewa don Allah ta zo.
“Bayan ta zu sai nace ta bani waya na kira malam don har yanzu bai dawo ba ko lafiya? Sai ta ba ni wayar na kira shi, sai ya ce telan ne bai hada mai kayan da wuri ba, amma yanzu ya Kawo Wanka zai hayo babur.
“To daga nan sai muka ci gaba da hira da budurwar tashi har dai yamma ta yi, so sai dai narakota na kara karbar wayar na kira sai ba ta tafiya muka yi ta kira ba ta zuwa.
“To sai muka yi sallama da ita ta tafi har dai dare ya yi sai na rufe kofa, sai da gari ya waye sai kawai yaro ya shigo ya ce mama ga babaca a hanyar Fawowa ayi mishi yankar rago,” in ji ta, daga nan Zulaihat sai ta fashe da kuka.
Makwabcin marigayin, Alhaji Ali Hadimi, shi ma ya yi karin bayanin cewa,” Mun sami Malam Salisu Kwance cikin jini kuma ko da muka duba ashe bayan sun kashe shi sun cire mazakutansa.”
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandar Jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, a zantawar su da wakilinmu, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce sun fara daukar matakan zakulo wadanda suka aikata wannan kisan gilla.