✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yanke masa hukuncin daurin wata 8 saboda satar jakar Kwamfuta

Wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa amma ya bukaci a yi masa sassauci.

Wata kotu a yankin Dei-Dei da ke Abuj ta yanke wa wani magidanci hukuncin daurin wata takwas a gidan yari bisa samun sa da laifin satar jakar kwamfuta.

Magidancin, wanda ke zaune a Gwarinpa, a Abuja ya amsa laifuka biyu da suka hada da sata da zamba cikin aminci, amma ya roki kotun da ta yi masa sassauci.

Sai dai alkalin kotun, Mista Sulyman Ola, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N40,000 sannan ya gargade shi da ya daina aikata laifuka.

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Mista Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara mai suna Ohanatu Sandra daga Rukunin Gidajen Brick City a Kubwa, ta kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Gwarinpa a ranar 3 ga watan Agusta.

Ogada ta ce da misalin karfe 2:20 na rana wanda ake tuhuma ya shiga ofishinta, ya sace jakar kwamfuta dinta dauke da kwamfuta guda hudu da kudinsu ya kai N280,000, sai zobe wanda kudinsa ya kai N80,000 da kuma tsabar kudi N300,000.

Mai gabatar da kara ya ce a yayin binciken ’yan sanda an kwato jakunkunan daga hannun wanda aka yanke wa hukuncin amma bai iya bayar da gamsasshen bayani kan abin da ya aikata ba.

Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 348 da 288 na kundin laifuffuka.