✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura wani mutum gidan yari kan dukan mahaifiyarsa a Gombe

A Litinin da ta gabata ce Alkalin kotun yanki ta Unguwar Bolari a jihar Gombe, Garba Abubakar Dule ya tura wani mutum mai suna Adamu Maigari…

A Litinin da ta gabata ce Alkalin kotun yanki ta Unguwar Bolari a jihar Gombe, Garba Abubakar Dule ya tura wani mutum mai suna Adamu Maigari mai shekara 40 da haihuwa da ke zaune a Unguwar Pantami zuwa gidan yari kan dukan mahaifiyarsa, Maryam Maigari.

’Yan sanda sun gurfanar da Adamu Maigari ne a gaban kotun bisa aikata laifin dukar mahaifiyarsa da ya yi a gaban kannensa da misalin karfe goma sha biyu na daren ranar Juma’a da kuma yi mata barazanar kisa.

Shi dai Adamu ya aikata laifin da ake zarginsa ne a ranar Juma’a 10 ga watan Mayu inda a gaban kannensa ya daki mahaifyarsu ya kuma ce sai ya kashe ta, wanda hakan ya sa a ranar Litinin aka gurfanar da shi a gaban Alkalin kotun Yanki ta Bolari.

Dan sanda mai gabatar da kara Sarjan Hassan Muhammad ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba dokar kasa sashe na 155 da 396 na kundin laifuffuka da hukuncin kotun.

Da kotu ta tambayi wanda ake karar don jin ta bakinsa game da laifin da ake zarginsa a kai, nan take ya amsa laifinsa, wanda hakan ya sa Alkalin kotun ya tura shi zuwa gidan yari kafin ranar da za a ci gaba da sauraron karar, wato 6 ga watan Yuni.