✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura sojojin Nijeriya 177 aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

Ana fama da matsalolin shugabanci a Guinea-Bissau lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar Yammacin Afirka.

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da tura jami’anta 177 domin aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasar Guinea-Bissau a wannan Larabar.

Shugaban sashen gudanarwa na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Manjo Janar Boniface Sinjen, ne ya bayyana haka ranar Laraba lokacin bikin yaye sabbin sojojin musamman na tallafa wa ayyukan ƙungiyar ECOWAS a cibiyar horas da sojoji ta Jaji da ke Kaduna.

Yayin da yake jawabi ga dakarun kafin tafiyarsu zuwa Guinea-Bissau, Manjo Janar Sinjen, ya ce ƙasar — wadda ke yammacin Afirka na fama da matsalolin shugabanci, lamarin da ka iya haifar da barazana ga zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.

Ya ƙara da cewa aika dakarun zuwa Guinea-Bissau da gwamnatin ƙasar ta yi ta hanyar ƙungiyar ECOWAS ya nuna irin goyon bayan ga Najeriya ke bai wa kasar domin maido da ƙimarta, tare da magance matsalolin da ta fuskanta da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyyarta da kuma wanzar da zaman lafiyar ƙasar.

“Ya ku mazajen sojoji, an ba ku cikakken horo a wannan gida domin taka wannan muhimmiyar rawa.

“Wannan horon da aka yi muku zai ba ku damar amfani da dabaru da ilimin da za ku taimaka wa gwamnatin Guinea-Bissau wajen daidaita ƙasar.

“Ina umartar ku, da ku zama jajirtattun dakaru wajen wannan gagarumin aiki na wanzar da zaman lafiya, ƙarƙashin inuwar ECOWAS.

“Za ku yi aiki ne a ƙasar da ke fama da rikicin ƙabilanci, don haka sai kun jajirce.

“Za ku yi aiki a cikin yanayi mai sarƙaƙiya da banbance-banbance, inda ƙabilu daban-daban ke zama tare.

“Don haka ina roƙonku da ku ci gaba da jajircewa wajen kiyaye mutunta ’yancin ɗan Adam da ƙa’idojin ayyukan wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar ECOWAS,” in ji shi.