An tsinci gawar wani yaro dan shekara 8 a gefen rafi a Zariya, kuma ake zargin cewa an kwakule idanunsa tare da yanke mazakutansa da harshensa.
Aminiya ta gano cewa yaron mai suna Ibrahim Muntaka Muhammad sun zo gidan kanwar mahafiyar ne bukin yayansa a unguwar Gaskiya Layout daga Kano, amma aka neme shi aka rasa tun da misalin karfe hudu na yammacin Laraba.
Majiyar ta ci gaba da cewa an kai cigiyar sa duk inda ya kamata amma ba a ganin shi ba har gari ya waye.
A safiyar Alhamis din nan ne aka tsinci gawarsa a gefen Rafin Kwarin Dan Goma, jini na fitowa daga idanunsa da bakinsa.
- Zamfara: An rufe kasuwanni 11 kan hulda da ’yan bindiga
- Soja ya kashe direban kayan agaji kan na-goro a Borno
Labari dai ya karade gari cewa an tsinci gawar ce an riga an kwakule idanun Ibrahim, an kuma yanke mazakutarsa da harshensa a lokacin da aka ga gawa.
Hakan ta sa wakilin Aminiya ya ziyarci gidan da yaron suka zo a unguwar Gaskiya Layout, inda ya tarar an riga an yi wa gawar wanka.
Amma duk da haka iyalan sun ba shi izinin duba gawar yaron tare da daukar hotonsa, kuma ya ga babu abin da aka yanka na jikin yaron.
Mijin kanawr mahaiyar yaron wanda ya wakilci iyayen yaron, Farfesa Aminu Muhammed Kutugi, wanda likitan ne a tsangayan koyar da likitanci a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya tabbatar cewa babu wani sashi na jikin yaron da aka cire, kuma ya yi kira ga jama’a da su daina yada abin da ba su da tabbaci a kai.
Shi ma Limam Muhammad Sani Abdurrahaman, wanda shi ne ya yi wa yaron wanka ya karyata batun cewa an kwakule idanun yaron ko yanke mazakutansa.
Liman Muhammad Sani ya ce, jini ne dai kawai yake fita daga idanun yaron da bakinsa da kuma kasar cibiyarsa, amma babu wani abu da aka cire a jikin gawar yaron.
Wannan lamari dai ya jefa mutanen yankin cikin dimuwa da alhini, inda suka fara addu’ar Allah Ya kawo karshen irin wannan rashin imani, Ya bayyana duk masu hannu a ciki.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da tsintar gawar yaro, kuma ya ce a abin da likitoci suka tabbatar musu, shi ne cewa babu abin da aka cira a jikin yaron, kuma suna kokarin gano ainihin abin da ya faru da yaron.