✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar yaro a bakin rafi a Kano

An tsinci gawar yaron a bakin wani rafi a yashe.

An tsinci gawar wani yaro mai shekara 14 da rana bayan ya nutse a ruwa a Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar a ranar Litinin, ta wata sanarwa da kakakinta , Saminu Yusuf Abdullahi, ya fitar.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 3.27 na rana daga wani mai suna Muhammad Adamu, nan take muka tura jami’anmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 3:32 na rana.”

Sanarwar ta kara da cewa an kai yaron da aka tsinci gawarsa a ranar Litinin babban asibitin Muhammadu Sunusi domin kula da lafiyarsa, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Abdullahi ya kara da cewa, an mika gawar ga ASP Abdul’aziz Sani na caji ofis din Dakata domin gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.