✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar wata da ake shirin aurenta da magidanci a cikin mota a Kano

An yi kicibus da gawar wasu mutum biyu, mace da namiji da aka tsinto cikin wata mota daura da titin Katsina da ke Karamar Hukumar…

An yi kicibus da gawar wasu mutum biyu, mace da namiji da aka tsinto cikin wata mota daura da titin Katsina da ke Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Wani shaidar gani da ido ya zayyana wa wakilinmu cewa, gawar mutanen da aka tsinto ta wani magidanci ce mai ‘ya’ya biyu mai suna Steven Ayika da kuma ta wata mai suna Chiamaka Emmanuel, da ake shirin bikin aurenta a watan Dasimba na gobe.

Bayanai sun ce an tsinto gawara mutanen biyu a cikin wata mota mai bakin gilasai a kofar gidansu marigayiyar da ke kan titin na Katsina.

Majiyar ta ce an rufe motar daga ciki kuma duk wayoyin mutanen biyu da suka riga mu gidan gaskiya duk an same su a rufe.

Wata majiyar ta ce jami’an ‘yan sanda sun samu gawar mutanen biyu a wani yanayi na kusanci da juna.

Da yake tabbatar da lamarin, Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tawagarsu tuni ta isa wurin bayan samun rahoton da ya ankarar da ita a kan lamarin.

DSP Kiyawa ya ce bayan an garzaya da mutanen biyu asibiti likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.

Ya ce a halin yanzu bincike ya kankama inda za a ci gaba da gudanar da shi har sai an ga abin da ya turewa buzu nadi.