✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar shahararren ɗan daudu a Abuja

Da alama an ji wa Area Mama rauni a fuskarsa yayin da aka samu kayansa duk a watse a gefensa.

An tsinci gawar wani shahararren ɗan daudu mai suna Area Mama a kan hanyar unguwar Katampe zuwa Mabushi a Abuja, ranar Alhamis.

A cikin wani hoto na ɗan daudun da aka yi ta yaɗawa yana kwance, an tsinci shi a cikin jini tare da tabo a jikinsa.

Da alama an ji wa Area Mama rauni a  fuskarsa yayin da aka samu kayansa duk a watse a gefensa.

Kwamishinan ‘yan sanda a babban birnin tarayya, Benneth Igweh, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar ɗan daudun.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh ta fitar, ta ce da sanyin safiyar ranar ne rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa game da lamarin.

Adeh ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa namiji ne sanye da kayan mata, kuma babu wata alama da za ta nuna ko wane ne shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Sakamakon kiran da rundunar ‘yan sandan ta samu a ranar 08/08/2024 da misalin ƙarfe 07:40 na safe, an ga wata mata da ba a san kowace ce ba tana kwance ba ta motsi a kan titin Katampe zuwa Mabushi, nan take aka aike da jami’an ‘yan sanda zuwa wurin.

“Bincike na farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin namiji ne da ke sanye da kayan mata kuma babu wata alama da za ta nuna ko wane ne shi.

“Nan take aka kai shi asibitin gundumar Maitama inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da rasuwarsa.

“Kwamishanan ‘yan sandan Abuja, CP Benneth C. Igweh, psc, mni, ya ba da umarnin gudanar da sahihin bincike cikin hikima don bankaɗo al’amuran da suka shafi mutuwarsa.”