✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar mutum 46 da ke son tsallakawa Amurka ci-rani daga Mexico

Ana tunanin zafi ne ya kashe mutanen a cikin motar

Akalla ’yan ci-rani masu son tsallakawa Amurka daga kasar Mexico 46 ne aka tsinci gawarsu a cikin wata lalatacciyar babbar mota a wajen garin San Antonio na Jihar Texas ta Amurkar.

Wani jami’in hukumar kashe gobara a Jihar ta Texas ya ce akwai kuma wasu mutum 16, ciki har da mata da kananan yara da aka garzaya da su asibiti, saboda rashin lafiyar da suke fama da ita sakamakon tsananin zafi.

Garin San Antonio, mai nisan kilomita 250 daga kan iyakar Amurka da Mexico, wata babbar mashiga ce da ’yan ci-ranin ke amfani da ita wajen safarar mutane zuwa Amurkan ba bisa ka’ida ba.

Magajin Garin San Antonio, Ron Nirenberg ya ce, “Wadannan mutanen na da iyalai, kuma bisa ga dukkan alamu na kokarin samun ingantacciyyar rayuwa ne. Wannan mummunan labari ne gaskiya.”

Mahukuntan garin sun ce ma’aikata sun kai dauki ne bayan sun ji ihun mutane na neman taimako daga wajen.

Direban motar ne dai ya tafi ya bar ta ba tare da iskar shaka ko ruwan sha a cikinta ba, kuma ma’aikatan ceto ba sa tsammanin samun mutane a cikinta.

Ana fama da matsanancin zafi dai a garin na San Antonio a ’yan kwanakin nan, wanda yakan kai kusan 39 a ma’aunin Celsius, inda ake zargin shi ne ma ya kashe su.

Ministan Harkokin Wajen Mexico, Marcelo Ebrard, ya ce daga cikin mutum biyun da aka kai asibitin har da ’yan kasar Guatemala guda biyu.

Sai dai ba a kai ga tantance ko ragowar mutanen ’yan wacce kasa ba ne.

Tuni dai aka kama mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin wadanda aka damka su ga gwamnati yayin da ake ci gaba da bincike.