Mazauna rukunin gidajen ‘World Bank’ dake Umuahia, babban birnin jihar Abiya, sun wayi gari da ganin gawar wani matashi a cikin bola bayan an kashe shi.
Gawar matashin ta nuna alamun an gana masa azaba kafin a kashe shi, saboda harbin bindiga dake jikinsa da kuma kansa.
- Kifi zabiya mai ido daya ya firgita masunci
- Kotun Kolin Indiya ta share hanya ga mabiya addinin Hindu su gina wajen bauta a filin Masallacin Ayodhya
- ’Yan sanda sun budewa mabiya shi’a wuta a Abuja
Mutanen da ke fita wurin ibada da sanyin safiya ne suka fara hangen gawar matashin kwance cikin jini a wata bolar yankin.
Daga nan ne mutane daga masu wucewa da ma mazauna rukunin gidajen suka fahimci abin da ke faruwa.
Sai dai har yanzu ba a kai ga gano wadanda suka kashe matashin ba, ko da yake wasu na zargin ’yan kungiyar asiri, ’yan bindiga ko kuma masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi.
Har wa yau, babu wanda zai iya bayyana lokacin da aka kashe matashin, amma ana tsammanin an kashe matashin ne a wani waje sannan aka yar da gawar tasa a yankin.
Da misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata ne, aka hangi jami’an ‘yan sanda sun isa waje gawar inda suka gudanar da bincike.
Ya zuwa wannan lokaci da muke gada wannan rahoto, an kasa samun kakakin ‘yan sandan jihar, Mista Geoffrey Ogbonna, don tabbatar da faruwar lamarin.