An tsinci gawar wani matashi mai kimanin shekara 12 da haihuwa da ake zargin matsafa ne suka kashe shi tare da cire wasu sassan jikinsa a bayan dutsen Madarkachi da ke cikin birnin Zariyan Jihar Kaduna.
An tsinci gawar matashin mai suna Sulaiman Aminu Saleh ne ranar Litinin.
- Yadda Jihar Legas ta samar da kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a Afirka
- Kotu ta daure matashi shekara 4 kan satar ‘pampers’
Da yake bayani kan aukuwar lamarin mahaifin yaron, Aminu Saleh Mohammed, ya ce tun ranar Lahadi Sulaiman ya bace lokacin da aka aike shi karbo cajin waya, bai dawo gida ba.
Ya ce tun daga nan sai suka fita nemansa a duk inda ake zaton zai je har karfe 12:00 na dare ba su gan shi ba.
A cewarsa, “Ko da gari ya waye da safiyar Litinin sai suka ci gaba da nemansa, amma ba mu gan shi ba sai da Magaribar ranar Litinin sannan aka kira ni a waya aka sanar da ni cewa na zo gida an ga gawar yarona.”
Ya ce wadanda suka saci yaron sun yi kaca-kaca da gawarsa ta hanyar cire gabansa da idanuwansa da harshensa.
Mahaifin ya kuma ce an sossoka masa wuka a baya sannan sun kuma karya masa kafa da kuma buga masa makami a ka.
Malam Aminu Saleh bayan da ’yan sanda suka dauki gawar suka yi rubuce-rubucen da za suyi, sai ya bukaci da a ba shi gawar yaronsa domin su yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kuma suka amince suka ba shi.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar, DSP Muhammad Jalige, ya ce ’yan sanda sun dukufa wajen bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin su fuskanci hukunci.
Jalige ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya bukaci jama’a da su rika sanya ido a kan abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma tare da bayar da rahoto ga rundunar domin daukar matakin gaggawa.
Ko a shekarun baya, an taba kwakule wa wani yaro idanu a anguwar Ban Zazzau da ke Zariyan.