✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar mai ciki a gefen titi a Kano

Saurayinta da abokinsa sun kashe ta bayan gaza zubar da cikin da ta ke dauke da shi.

An tsinci gawar wata mai ciki mai shekara 20 a gefen titi a kauyen Anadariya a Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana haka ne a ranar Talata, inda ta ce an tsinci gawar ne a ranar 28 ga watan Maris.

A cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce an cafke wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan matar.

Ya ce kamen na zuwa ne kwanaki kadan da kisan nata bayan da wasu mazauna yankin suka shigar da kara kan lamarin kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda ya turo jami’an ‘yan sanda wurin.

“Da samun rahoton faruwar lamarin Kwamishina Mamman Daura ya aike da tawaga wajen karkashin jagorancin SP Tanimu Wada da ke ofishin ‘yan sandan na Bebeji.

“Bayan isa tawagar sun dauki gawar zuwa Babban Asibitin Tiga, wanda a nan aka tabbatar da rasuwarta.”

Kakakin ya ce an gano sunan matar a matsayin Theresa Yakubu, kuma an cafke saurayinta da abokinsa.

Saurayin nata ya amsa cewar sun kashe ta shi da abokinsa bayan ya yi mata ciki, kuma sun yi yunkurin zubar da cikin amma abun ya ci tura.