✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar mace da aka yi gunduwa-gunduwa da ita a Indiya

Ana zargin an yi matar gunduwa-gunduwa, bayan yanke al'aurarta, ne domin tsafin neman kudi.

’Yan sanda a kasar Indiya sun gano gawar wata mata da aka yi gunduwa-gunduwa da ita wanda ake zargin aikin matsafa ne.

Ana zargin an an makure matar an kashe ta ne, sannan aka yi gunduwa-gunduwa da gawarta, bayan an yanke al’aurarta, domin yi wa wasu ma’aurata tsafin neman kudi.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a yankin Kochi, S. Sasidharan ya ce, suna kan binciken duka mutum ukun da aka kama, cikin har ma’auratan da ake zargin suna da hannu a kisan wasu mata biyu a yankin.

Binciken hukuma ya gano matar, wacce ke aikin sayar da tikiti a wani gidan caca, an yaudare ta ne zuwa inda aka kai ta aka kashe gidan ma’auratan.

Tun farko, Kotun Kochi ta ba da umarnin ’yan sanda su ci gaba da tsare wadanda ake zargin na tsawon kwana 12.

’Yan sandan sun ce, ba su tsayar da rana da kuma lokacin da za su karbi shaidu a kan batun ba, amma nan ba da dadewa ba za su yi matsaya a kansu.

Sun ce akwai jita-jita da yawa a kan kisan wanda akwai bukatar su gudanar da bincike mai zurfi don gano gaskiya.