An tsinci gawar wata mace da aka yi wa gunduwa-gunduwa da ita a karkashin Gadar AYA da ke Abuja.
Wani ganau mai suna Shedrack ya ce an tsinci gawar ce da misalin karfe 5 na asuba ranar Asabar kuma ana zargin matsafa ne suka jefar da ita a karkashin gadar.
- Gwamnatin Zamfara ta soke nadin sarautar kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiro
- Samar da makamai ga jama’a don kare kai: A jaraba tsarin Zamfara
Ya ce wasu motoci da ke tahowa ta bangaren Nyanya sun bi ta kan gawar, don haka ba a iya gane mamaciyar ba.
Gadar AYA da ke Abuja na kan hanyar da ta dangana da Nyanya har zuwa Keffi a Jihar Nasarawa.
Kakakin ’yan sanda ta Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa wakilinmu cewa jami’an rundunar sun tsinci gawar wasu mata biyu a wurin.
Josephine ta bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna masu ababen hawa ne suka kade su sannan suka tsere.
Ta ce bayan samun kiran gaggawa ne Babba Ofishin ’Yan sanda da ke yankin Asokoro a Abuja ya tura jami’ansa wurin suka dauke gawarwakin.
Bayan zuwa asibiti ne likitoci suka tababtar da mutuwar matan sannan aka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa na Asokoro.
Ta bayyana cewa sun riga sun fara bincike domin cafko wadanda suka aikata laifin, kuma an riga an tuntubi iyalan mamatan.