✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar dan sanda a Abuja

An gano ya rasu lokacin da aka je tashin sa da nufin zuwa sallar Juma'a.

An tsinci gawar wani mataimakin Sufetan ‘yan sanda (ASP), Salisu Garba Zuba a gidansa da ke Zuba Karamar Hukumar Gwagwalada ta babban birnin tarayya Abuja.

Wani dan uwan mamacin mai suna Adamu Garba, ya ce jami’in ya rasu ne jim kadan bayan ya dawo daga aiki a daren ranar Alhamis a ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada.

Ya ce Zuba na cikin koshin lafiya lokacin da ya dawo daga wurin aiki, amma ya ce bayan ya shiga dakinsa da nufin hutawa sai mai aukuwar ta auku.

Dan uwan nasa ya ce sun tsinci gawarsa lokacin da aka je tashinsa domin yin sallar Juma’a.

Ya kara da cewa an garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa, kuma tuni yanzu an birne gawarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Aminiya ta samu labarin cewa marigayin mai shekara 42 a duniya, wanda dan kabilar Koro ne, ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai.