✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsige Shugaban Majalisar Imo

Majalisar Dokokin Jihar Imo ta tsige Shugabanta, Chiji Collins saboda zargin almundahana. ’Yan Majalisar sun zabi Paul Emeziem daga Karamar Hukumar Onuimo a matsayin sabon…

Majalisar Dokokin Jihar Imo ta tsige Shugabanta, Chiji Collins saboda zargin almundahana.

’Yan Majalisar sun zabi Paul Emeziem daga Karamar Hukumar Onuimo a matsayin sabon Shugabansu.

Mutum 19 daga cikin ’yan Majalisa 27 ne suka tsige Chiji Collins a zaman Majalisar na ranar Juma’a.

Sauran zarge-zargen da ya sa takwarorin Chiji Collins suka tsige shi sun hada da yin karfa-karfa da kuma saba ka’idojin aiki.