Jama’a sun yi ta tserewa bayan samun labarin yiwuwar ’yan bindiga za su kawo musu hari a kasuwa a yammacin Juma’a.
Mutane a Babbar Kasuwar Markurdi, sun yi ta kafa-me-na-ci-ban-ba-ki ba, bayan jin rade-radin cewa ’yan bindiga na shirin kai hari kasuwar.
Bazuwar labarin ya haifar da rudani a Kusuwar, inda mutane ke cewa rashin daukar ire-iren labarin da muhimmanci a baya ne ya kai ga halaka mutane a yankunan da ke kusa da kasuwar.
Baya ga masu saye da sayarwa da suka yi ta arcewa daga kasuwar, masu sana’ar haya da ababen hawa ma sun dauke kafa daga yankin da ke babban birnin na Jihar Binuwai.
Kan ka ce kwabo, ’yan kasuwa a kasuwannin Wadata da kuma High Level da ke garin na Markurdi suka shiga rufe kantuna suka koma gida saboda gudun abin da ka je ya dawo.
Wani ganau ya ce yawaitar hare-hare a kwanakin baya a kan hanyar Makurdi zuwa Naka da ke daura da kasuwar na daga cikin dalilan fargabar.
Ya ce a hare-haren na baya mutane sun yi watsi da jita-jitar da suka ji, sai kuma ta tabbata, har aka yi asarar rayuka da yawa.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto an tuntubi Rundunar ’Yan sandan Jihar Binuwai, amma kakakinta, DSP Catherine Anene, ba ta iya tabbatarwa ba.
Amma wakiliyarmu ta ga jami’an ’yan sanda da yawa suna kai-komon sintiri a babbar kasuwar domin tabbatar da tsaro.