Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta tsare wasu jami’anta biyar da suka yi sanadin mutuwar wani matashi dan shekara 17, Ibuchim Ofezie a Jos.
Kakakin rundanr ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce za a hukunta jami’an da zarar an kammala bincike kan zargin kisan matashin.
- Mutum uku sun rasu a hatsarin mota a hanyar gidan gwamnatin Kano
- NAJERIYA A YAU: Yadda kalaman Abba Gida-gida ke yamutsa hazo a Kano
“An ruwaito cewa a kokarin hana sana’ar acaba a jihar, jami’an sun kai samame don kama wadanda suka karya dokar wanda hakan ya sa suka dinga harbi a iska lamarin da ya sanya harsashi ya samu Ofezie a cikin shagonsa a kasuwa.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bartholomew Onyeka ya yi Allah wadai da kisan matashin mai shekara 17 mazaunin yankin Agingi a Karamar Hukumar Bassa.
“Kwamishinan ya bayyana lamarin a matsayin abun damuwa, yana mai cewa an samar da ‘yan sandan ne don su tabbatar da doka da kuma kare rayukan jama’a ba su kashe ba.
“Ya bayar da umarnin tsare jami’an tare da gudanar da bincike.”
Tuni aka tsare jami’an ‘yan sandan biyar da ake zargi a sashen binciken manyan laifuka na SCID da ke jihar.