✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare mutumin da ya sa a yi garkuwa da matarsa a gidan yari

Jami'an tsaro sun zargi magidanci da hada baki wajen yunkurin sace matarsa.

Wata kotu ta ba da umarnin tsare wani magidanci da ya hada baki da wasu mutane da su yi garkuwa da matarsa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta gurfanar da mutumin ne bayan matarsa ta kai koke ga Rundunar game da yunkurin yin garku wa da ita

A don haka aka gurfanar da shi ne a gaban Majistare da ke zamanta a Ilorin bisa zargin hada baki da wani mai maganin gargajiya da wasu mutane biyu su yi garkuwa da matar tasa.

Dan sanda mai shigar da kara, Sajan Abubakar Issa ya shaida wa kotun cewar bincike ya gano yadda mijin matar ya kira wani a wajen da aka yunkurin sace ta.

An kuma gano wani mai maganin gargajiya da wasu mutane da suka nemi yin garkuwa da ita ba tare da nasara ba, wanda ya sa ta shigar da kara bisa zargin yunkurin garkuwa da ita.

Dan sandan ya saida wa kotun cewa hakan laifi ne a karkashin sashe na 97 274 na kundin laifukan jihar.

Alkalin Kotun, Afusat Alege ya ba da umarnin tsare magidanci a gidan yari na Oke-Kura da ke birnin Ilorin.

Sannan ya dage zaman har zuwa ranar 24 ga Fabrairu don ci gaba da sauraren shari’ar.

Sai dai mijin natar da ragowar wanda ake tuhumar a gaban kotu, duk sun musanta zargin da ake musu.