Wata mata da ke musguna wa diyar kishiyarta mai shekara takwas ta shiga hannun hukuma tare da uban yarinyar.
An kama tare da tsare matar da mijinta wanda suka dade da rabuwa da mahaifiyar yarinyar ne bisa jagorancini cibiyar sauraron koken cin zarafin mata da kananan yara na Salama da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar da rundunar jami’an tsaro ta Sibil Difens (NSCDC).
“Abun takaicin shi ne yadda mahaifin yarinyar ya hada kai da kishiyar uwar suna musguna wa yarinyar, ga jikinta nan, kana gani duk alamar duka”, inji shugabar cibiyar, Misis Grace Abbin.
Da take karin haske bayan ta gabatar wa Aminiya yarinyar a ofishinta, Misis Grace ta ce sun samu korafin ne daga makwabta kan yadda matar take gallaza wa yarinyar da takura da wahalarwa.
Ta ce an saki matar amma ana ci gaba da rike mahaifin yarinyar saboda matar tana da jaririya mai wata biyu da take shayarwa.
“Za mu ci gaba da bincikar sa tukuna kafin daukar mataki na gaba a kan sa”.
Ta ce cibiyar za ta ci gaba da kwato wa yara da mata hakkinsu domin a cewarta, babu inda al’umma za ta je matukar ana take hakkin musamman kananan yara.
A yanzu haka yarinyar na ci gaba da samun kulawa a Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan inda ta fara murmurewa.