✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsare malamai 6 kan tilasta wa dalibai kwaikwayon jima’i a Kenya

Daya daga cikin malaman namiji ne sauran kuma mata

Rahotanni daga kasar Kenyan sun ce an tsare wasu malaman makarantar firamare su shida bayan da suka tilasta wa wasu dalibansu kwaikwayon jima’ai a matsayin horo.

’Yan sandan yankin sun fada a ranar a Alhamis cewa sun tsare malaman ne bayan ganin bidiyon da aka yada a kafoin sada zmunta na abin da suka aikata.

Bidiyon ya nuna yadda wasu dalibai hudu na kwaikwayon jima’i a karkashin wata bishiya da ke harabar makarantar yayin da malaman kuma suka tsare su da kallo har da dariya.

An nado yadda aka sanya, “yara akaita halin rashin kunya” a kauyen Nyamache, mai nisan mil 186 daga Nairobi, babban birnin kasar,” in ji ”yan sanda.

Sun kara da cewa, wadanda aka tsaren na taimaka musu wajen bincike.

Kafar AFP ta ce daya daga cikin malaman da lamarin ya shafa namiji ne sauran kuma mata.