Wata kotun majistare ta tsare wani a gidan yari bayan samun shi da laifin satar rigar wata bakuwa a otal din da yake aiki.
Alkalin kotun da ke zamanta a Legas, M. I. Dan-Oni, ya bayar da umarnin tsare matashin a gidan gyaran hali na Ikoyi har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci.
- AFCON: Yadda alkalin wasa ya hura tashi lokaci bai yi ba
- Muddin ba a tashi tsaye ba, mayakan ISWAP za su fitini Najeriya —Zulum
Dan-Oni ya kuma dage zaman kotun har zuwa ranar 14 ga watan Janairun da muke ciki don ci gaba sauraren shari’ar.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara gaban kotun, Isfekta Courage Ekhurorohan, ya shaida wa kotun cewa matashin mai shekara 21 ya aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Disamba 2021, a otal din Rita Lori da ke unguwar Surulere a Legas.
Ekhurorohan ya ce wanda ake tuhumar ya saci riga a dakin wata bakuwa da kuma wani firinji wanda kudinsa ya kai N375,000 a otal din.
Ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba da sashi na 287 na kundin laifuka na Jihar Legas na 2015.
Sashin na 287 ya tanadar da hukuncin daurin shekara uku ga wanda aka kama da laifin aikata sata.