Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta tsare wani jami’inta mai suna Victor Oshabuohign da aka nada cikin wani hoton bidiyo yana karbar kudi daga hannun wani mutum mai suna Bolu a garin Benin.
Da take magana da manema labarai a Benin, kakakin ‘yan sandan jihar, Jenifer Iwegbu, ta ce an kama jami’in da ke cikin hoton bidiyon wanda yanzu haka ake gudanar da bincike a kansa.
- Yayar tsohon Shugaban Kasa Yakubu Gowon ta rasu
- Najeriya ga kamfanin Google: Ku hana IPOB amfani da dandalinku
“An jawo hankalin rundunar a kan wani hoton bidiyo da ke yawo a Twitter, wanda ya nuna jami’an ‘yan sanda suna tattaunawa da wani mai abun hawa mai suna Bolu a dandalin sada zumunta.
“An kama jami’in mai lambarsa ta aiki F/No 524971 PC Victor Oshabuohign, dan sandan da ke cikin hoton bidiyon, an tsare shi kuma a halin yanzu ana kan bincike.”
Ta bayyana cewa wasu jami’ai shida, ASP God’spower Ijebu, Insifekta Ebatamole Philip, Insifekta Inaite Vincent, Insifekta Ademola Benjamin, Insifekta Robert Esikise da Insifekta Adefaye Samuel da aka kama tun da farko kan zargin cin hanci da rashawa, wanda suna jiran hukunci.
Ta ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Abutu Yaro, ya kafa kwamitin bincike karkashin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, ACP James Chu, a wani bangare na kokarin binciken duk wasu al’amuran da suka shafi cin hanci da rashawa na ‘yan sandan da aka tsare.
A cewarta, za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanadar.