Kwamatin aurar da zawarawa na karamar Hukumar Kafin Hausa ya mika rahotan sunayen zawarawan da ya tantance ga babban kwamatin tantance zawarawa na Jihar Jigawa, domin yi wa wadanda aka tantancen aure kamar yadda Gwamnatin Jihar ta ba da umarni.
Kwamandan Hisba na karamar hukumar, Malam Abdulrazak D. Zakari ya sanar da Aminiya haka bayan tantance yawan zawarawa a karamar hukumar ta Kafin Hausa a kwanakin baya.
Ya ce kwamatin ya tantance mata 81 da suka hada da sunayensu da bayanansu da kuma tabbatar da koshin lafiyarsu, kamar yadda aka gindaya dukkanin sharuddan auren a cikin jadawalin da gwamnatin jihar ta bayar. Ya ce akwai ragowar mata takwas da ba su sami wadanda za su aure su ba, haka kuma an sami maza guda shida da su ma ba su sami matan da suke da bukatar aure ba.
Shugaban karamar Hukumar Kafin Hausa, Alhaji Haruna wanda Adamu Baban Barai ya wakilta a wajen taron tantancewar, ya gargadi mata da mazan da suka nuna sha’awarsu a kan auren su kasance masu tsoron Allah. Ya kuma shawarci dukkan bangarorin biyu su zama masu biyayya da juna, domin aure ibada ne, ba wata rayuwa ce kawai ta jin dadi ba.