Kwamitin Zakka da Wakafi na jihar Gombe ya ce ya kashe kimanin Naira miliyan 1.7 wajen tallafa wa gajiyayyu da marayu a fadin jihar.
Shugaban kwamiti na musamman kan harkar ciyarwa na watan Azumi Sani Rabi’u ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da Aminiya.
Sani Rabi’u ya ce Kwamitin zakka da wakafi ya tallafawa magidantan da basu da karfi kimanin su 80 da kayan abinci da marayu maza da mata da marasa galihu suma 80 da kayayyakin sallah da kuma kudin dinki.
Kayan abincin
Sani ya kuma ce kayan abincin da suka raba sun hada da: Shinkafa mudu 15 da gero mudu 10 da wake mudu 10 da suga mudu biyar da ledar magi uku da kuma man girki mai lita 5 gallon 1.
Marayu maza kuma an basu yaduna bibiyu wasu uku bisa ga shekarunsu mata kuma turmin zani da kudin dinki kowannen su Naira 1000 maza da matan.
A cewarsa kudaden da suka kashe tallafi ne da suke samu daga mambobin kwamitin da suke bayarwa fisabilillahi wasu kuma suna bada kashi biyu cikin dari na albashin su duk wata dan gudanar da aikin alheri irin wannan.
Yadda ake tara kudaden
Sani Rabi’u ya kara da cewa, bayan azumi ya wuce za su ci gaba da bai wa mata marasa galihu tallafi na jari kamar yadda suka saba na N10.000 suna juyawa duk bayan mako biyu suna kawo ribar da suka samu ana rabata gida uku a ajiye musu.
A cikin ribar kashi biyu cikin 100 a kara akan uwar kudin bayan wasu watanni sai a duba aga nawa kowacce ta ajiye sai a dauki kudin su a dunkule a basu su kara jarin dan dogaro da kansu.
Sannan idan mace tana da yaron da yake zuwa makaranta basa iya biya masa kudin makaranta ko na rashin lafiya daga dan abin da take ajiyewa za a cire wani kudi a bata dan ta biya.
Daga nan ya yi kira ga al’umma da su su hada kai da kwamitin zakka da wakafi wajen bada zakkar su ga kwamitin da kuma tallafin da ya dace dan gudanar da aikin Allah.