✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tallafa wa masu kananan sana’a’o’i da N100m a Konduga

Gwamnan ya ba da tallafin ne don farfado da harkar noma a yankunan da rikicin Boko Haram ya ritsa da su.

Gwamnatin Borno ta raba wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i tallafin miliyan Naira miliyan 100 a Karamar Hukumar Konduga.

Kaso 70 na wanda aka tallafawar sun fito ne daga Konduga, sai kaso 30 daga Auno, Dalori da Kawuri.

Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, wanda ya yi rabon kudin, ya gargadi wadanda aka ba wa da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Ya ce, gwamnatinsa na tallafa wa wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su ne don farfado da harkar noma a yankunan.

Kazalika, gwamnan ya raba wa hadin gwiwar jami’an tsaron jihar Naira miliyan 5.2 tare da alkawarin gyara musu ababen hawansu da suka lalace.