An sheka ruwa kamar da bakin kwarya a cikin yanayin damunar da aka dade ba a ga kamarta ba shekara 30 a kasar Chadi
Sakamakon haka, ruwan ya haifar da mummunar ambaliyar da shafe wasu unguwanni a Ndjamena, babban birnin kasar.
- Ambaliyar ruwa: An tsinci gawarwaki 15 cikin kogi a Maiduguri
- Yadda ambaliyar ruwa ta durkusar da kasuwanci a Kantin Kwari
A cewar kungiyoyin agaji da kuma hukumar kula da yanayi ta kasar, ambliyar ta tilasta wa dubban mutane barin gidajensu sama da wata guda da farawar damumar.
A unguwanni 18 da ke Ndjamena, ambliyar ta mamaye ko’ina, har ta kai a cikin kwalekwale ake iya motsawa daga wannan wuri zuwa waccan a cikin ruwan da ya kwanta tun karshen watan Yuli.
A cewar Hassan Hissien Acheik, wani mazunin birnin, “babu daya daga cikin unguwanni 18 na cikin Ndjamena da ambaliyar ruwan ba ta shafa ba, a wannan shekarar, abin bakin ciki ne da takaici”.
Rabon da kasar Chadi ta samu ruwan sama kamar haka, tun shekarar 1990, inji Idriss Abdallah Hassan, wani babban jami’in hukumar kula da yanayi ta kasar, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A ‘yan shekarun nan, mamakon ruwan sama da zaizayar kasa da kuma rashin tsara birane sun taimaka wajen samun yawan ambaliyar ruwa a wannan yanki na Afirka a cewar mujallar Notre Dame