An tafi da gawar Mai Martaba Sarkin Zazzau, Marigayi Alhaji Shehu Idris daga Kaduna zuwa Zariya a ranar Lahadi.
An dauki gawar mamacin ne a cikin wata farar motar daukar marasa lafiya daga Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna wadda ta samu rakiyar manyan jam’iyan gwamnatin jihar da masu rike da sarauta.
Wakilinmu ya ce an fice gawar basaraken ne ta tsohuwar kofar asibitin domin kauce wa taron jama’an da suka fara cincirindo a asibitin da ya rasu.
Tuni dai Gwamnatin Jihar Kaduna, ta bakin Gwamna Nasir El-Rufai ta sanar cewa za a yi jana’izarsa da misalin karfe biyar na yamma.
Da karfe 5 za a yi jana’izar Sarkin Zazzau —El-Rufai
Da Dumi-dumi: Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya rasu ne a ranar Lahadi 20 ga Satumba 2020 yana da shekara 84 a duniya.
Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu ne ya tabbatar wa Aminiya cewa Sarkin ya rasu ne da misalin karfe 12 a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna bayan fama da rashin lafiya.
Daya daga cikin sarakuna mafi dadewa a kan karaga, a watan Fabrairu ya yi bikin cika shekara 45 yana mulki.
An haifi Alhaji Shehu Idris ne a 1936, kuma ya rike mukamai da dama a Najeriya.
Daga cikin mukaman da ya rike akwai Shugaban Hukumar gidan Rediyo da Talabijin ta Jihar Kaduna (KSBC), da Darakta a Hukumar Gudanarwa ta kamfanin UAC.
Ya kuma yi aiki da Baitulamalin Hukumar En’e ta Zariya, da Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar Arewa a matsayin sakatare, sannan ya rike sarautar Danmadamin Zazzau Hakimin Zariya daga 1973 zuwa 1975.